Hukumar ‘yan sanda reshen jihar Kano ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi wajen ƙwacen wayar Likitan ƙashi Atiku Tijjani Shuaibu Rabo Ringim, wanda hakan yayi sanadiyar rasa ransa.
Mai magana da yawun hukumar DSP Abdullahi Haruna shi ne ya bayyanawa jaridar Vanguard a ranar Lahadi.
Idan ba a manta ba a ranar Alhamis ne da misalin ƙarfe 8 na dare masu ƙwacen wayar suka tare Rabo Ringim suka ƙwace masa wayar hannu tare da daɓa masa wuƙa a ƙirji.
Lamarin da yayi sanadiyar rasa ransa bayan kaiwa abokinsa ziyara dake unguwar Red Bricks kan titin Gwarzo a ƙaramar hukumar Gwale dake Kano.
Kafin rasuwar Rabo Ringim ya kasance ma’aikacin koyarwa na asibitin Malam Aminu Kano.
DSP Haruna yace wanda aka kama ɗin zuwa yanzu suna bada bayanan da zasu taimaka wajen cafko haƙikanin wanda suka aikata laifin.
Tuni dai mamacin aka masa sutura tare da birne shi a garin Ringim na jihar Jigawa kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.