Yayin da mutane da dama ke cece-kuce kan cewa waye ya fi dacewa namiji ya mutunta tare da dauka da kima tsakanin mahaifiyarsa da matarsa, wasu sun yanke shawara, LIB ta ruwaito.
KU KARANTA: Yadda nake samun N870k duk wata daga sana’ar wanke-wanke, Matashi
Duk da dai ko addini ya nuna matukar muhimmancin kulawa da iyaye tare da kyautata wa iyali, amma duk da haka akwai masu fifita matansu kan iyayensu.
Wani mai wasan barkwanci, Emmanuel Iwueke wanda aka fi sani da Craze Clown, ya bayyana cewa bai dace uwa ta zama mafi fifiko ba kan matar danta.
Ya fara da bayyana ra’ayinsa a shafinsa na Twitter inda yace:
“A matsayinki na uwa, idan har dan ki ya fifita ki a kan matarsa, to kin fadi a matsayinki na uwa.”
Duk da dai gajiyar wallafa ce, bai fadada bayani ba. Bai sanar da ta inda ya dace ace an fifita mata ba, ta bangaren kyautatawa ko kuma ta wani bangaren da ban.