Shugaban kasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, na shirin yin garambawul ga shugabannin gudanarwar kasar a ranar Litinin, a cewar kakakin sa, Vincent Magwenya a ranar Lahadi.
kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa Ramaphosa, wanda ya ninka a matsayin dan kasuwa, a halin yanzu yana zama shugaban kasa na biyar da aka zaba ta hanyar dimokradiyya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Idan Kuka Zabe Ni, Zan Biya Kowane Matashi Naira 30k Duk Wata — Dan Takarar Gwamnan SDP
An dai yi hasashen cewa za a yi wa majalisar ministocin garambawul tun bayan da aka sake zaben shugaban kasar a matsayin shugaban jam’iyyar African National Congress ANC mai mulkin kasar a zaben shugabancin jam’iyyar a watan Disamba, wanda ya share masa hanyar sake tsayawa takara a karo na biyu a shekarar 2024.
A wani taron manema labarai, Magwenya ya ce, “Shugaban yana kammala sake fasalin hukumar zartaswa ta kasa kuma yana yin la’akari da rantsar da wasu ‘yan majalisar kafin ya sanar da sauya shekar”.
Ana sa ran Ramaphosa zai nada sabon mataimakin shugaban kasa bayan fadar shugaban kasar ta sanar da murabus din David Mabuza daga mukamin sa a ranar Larabar da ta gabata. Sabon mukamin ministan wutar lantarki na daga cikin ayyukan da za a nada.
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: Tsohon Dan Majalisar Oyo Ya Rasu
Wani tsohon dan majalisar dokokin jihar Oyo, Tirimisiyu Okunola ya rasu.
Kanensa mai suna Bashir Okunola ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a shafin sa na Facebook.