Sau biyu Mata ta na haihuwa da wani – Ma’aikacin ruwa ya shaidawa Kotu
Wani ma’aikacin ruwa Desmond Igbo, a ranar Talata ya ja matarsa Rosemary, a gaban wata kotun gargajiya da ke Jikwoyi, inda ya zarge ta da haihuwar ‘ya’ya biyu ga wani mutum.
Mai shigar da karar wanda ke zama a karkashin ikon kotun, ya bayyana haka ne a cikin takardar sakin da ya shigar a gaban kotun.
KARANTA WANNAN LABARIN:Ɗangote na raba sinƙin biredi dubu 35,000 kullum a Kano da Legas
“Matata tana yin auren waje. Ta furta min cewa ɗana na biyu ne kaɗai ɗana da na haifa.
“Ta ce sauran biyun ba ’ya’yana ba ne.
“Na shafe shekaru 13 ina kula da su . Wannan abin baƙin ciki ne, game da wannan batu ne nake neman rabuwa da matata.” Yace.
Ya kuma shaida wa kotun cewa babu soyayya da fahimta a auren.
Wanda ake karar wadda ‘yar kasuwa ce, ta musanta zargin.
Mai shari’a, Thelma Baba, ta shawarci ma’auratan da su binciki yadda za a sasanta kuma ta dage ci gaba da shari’ar har zuwa ranar 25 ga wata, domin samun rahoton sulhu.
A wani labarin kuma:In kun sake ni, cikin mintuna 2 zan kawo ƙarshen rashin tsaro a Kudu maso Gabas – Nnamdi Kanu
Shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB, Nnamdi Kanu, ya sha alwashin kawo karshen rashin tsaro a yankin Kudu maso Gabas cikin mintuna biyu, idan aka sako shi daga inda yake a tsare.
Kanu ya ce a yankin Kudu maso Gabas babu wanda zai iya yin tir da umarninsa dangane da matsalar tsaro a yankin.