Gwamnan jihar Ebonyi Dave Umahi ya ce ya sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari burinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC mai mulki.
Matakin na Umahi ya zo ne sa’o’i 24 bayan jagoran jam’iyyar na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya dauki irin wannan matakin.
Gwamnan ya bayyana matakin nasa a baya-bayan nan ne ga manema labarai na fadar gwamnati bayan ganawar sirri da Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Talata.
Da aka tambaye shi ko me zai biyo baya bayan da wasu jiga-jigan ‘yan siyasa suka nuna aniyarsu ta tsayawa takara a wannan mukami ciki har da Asiwaju Tinubu, gwamnan ya ce Allah ne zai yanke hukunci kan sakamakon zaben.
Umahi, wanda ya bar jam’iyyar (PDP) zuwa APC, ya ce yana da dama idan APC ta jefa tikitin takara a bude.
Ya ce idan har ya samu dama, fadar sa za ta kwaikwayi kokarinsa a Ebonyi, yana mai cewa yana da abubuwa da yawa da zai iya nunawa wajen tafiyar da harkokin mulki a matsayinsa dan kasuwa.
Gwamnan ya kuma ce ya tattauna da shugaban kasar kan yadda za a magance matsalar tsaro da ta addabi yankin Kudu maso Gabas ta hanyoyin siyasa.