Shugaban Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila, ya taya kungiyar kwallon kafan Super Eagles ta Najeriya murnar nasarar da suka samu a kan Kasar Masar a wasansu na farko a rukunin D a gasar cin kofin nahiyar Afirka da aka yi a ranar Talata a Kamaru.
A cewar wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Lanre Lasis ya fitar, Gbajabiamila ya ji dadin yadda ‘yan wasan Super Eagles suka nuna bajintar da suka yi wajen kayar da kungiyar kwallon kafan kasar Masar, wadanda ake yi wa kallon daya daga cikin ‘yan wasan da aka fi so a gasar.
Shugaban majalisar wanda shi ne jagoran tawagar gwamnatin tarayya don faranta wa Super Eagles rai, ya lura da farin cikin kungiyar a tsakanin ‘yan wasan Eagles.
Ya bukaci ‘yan wasan Super Eagles da su ci gaba da kasancewa tare da su a duk lokacin gasar domin su dawo gida da kofin.
Gbajabiamila ya kuma yabawa kwararrun ma’aikatan Super Eagles da suka yi aiki mai kyau.
Ya kuma yabawa Ministan Matasa da Wasanni Sunday Dare da tawagarsa da kuma shugabannin hukumar kwallon kafa ta Najeriya.