Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, ya ce kafin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kare a shekara mai zuwa, kasar za ta dawo da martabar da ta ke a baya, inda za a samu zaman lafiya.
Ya kara da cewa shugaba Buhari yana aiki ba dare ba rana domin ganin an samar da dukkan hanyoyin da za a bi wajen mika mulki ba kawai a shekara mai zuwa ba, har ma da tabbatar da ganin an kawo karshen kalubalen da ake fama da shi na rashin tsaro a kasar nan.
Malami ya bayyana haka ne a ranar Asabar a lokacin da yake taya al’ummar Musulmi murnar bikin Sallar Idi na bana a Birnin Kebbi.
“Ina so in tabbatar muku cewa gwamnatin Buhari za ta ci gaba da yin duk mai yiwuwa don tabbatar da tsaron kasar nan. Ina addu’ar Allah ya amsa addu’o’inmu domin a samu dawwamammen zaman lafiya a jihar Kebbi da kasa baki daya, tare da samun canjin siyasa cikin kwanciyar hankali a farkon shekara mai zuwa,” inji shi.
A wani labarin kuma na daban
Matsalar Tsaro: APC tayi ga Ƴan Najeriya dasu yiwa Buhari addu’a
Jam’iyya mai mulki ta APC tayi kira ga ƴan Najeriya dasu yiwa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari addu’a akan matsalolin tsaro dake fuskantar Ƙasar.
A cikin sakon Sallah zuwa ga Musulmi a ranar Asabar, Sakataren Yaɗa Labaru na Jam’iyyar APC Barr Felix Morka yace ƴan Najeriya dole su sanya Najeriya farko a zuciyar su.
Jam’iyyar tace “muna kira ga Ƴan Najeriya dasu cigaba da goyon bayan Gwamnatin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari domin magance matsalar tsaro, tare da cigaba jefa da duk wani yunƙuri na siyasantar da Matsalar Tsaro a Kasar.
“A wannan lokaci na Bikin Babbar Sallah, muna kira ga Musulmi dasu cigaba da addu’a domin samun zaman lafiya da tsaro a ƙasar, a yayinda gwamnatin APC ke cigaba da bada fifiko ga jindaɗin ƴan Najeriya.
“A wannan lokaci muna kira ga ƴan Najeriya dasu sanya Najeriya farko a dukkanin lamurran su. Ba zamu daina yakar wanda suke Son suga sun rabamu da hanyar tsana