Wata budurwa ƴar Najeriya mai rayuwa a ƙasar Faransa ta bayyana halin matsin da take ciki na rashin samun abokin rayuwa.
Budurwar ta bayyana cewa a shirye take ta riƙa gwangwaje duk saurayin da zai aure ta, da albashi mai tsoka. Shafin Yabaleftonline ya rahoto.
KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sanya shugaba Buhari yayi shiru kan zarge-zargen da ake yiwa INEC -Fadar Shugaban Ƙasa
A wani bidiyo da ya yaɗu, budurwar wacce shekarun ta sun fara ja ta bayyana cewa tana ta tsufa gashi har yanzu ta kasa samun abokin rayuwa.
Ta yi iƙirarin cewa ta mallaki kadarori masu yawa a Najeriya da Faransa, sannan abu ɗaya kawai da ta rasa a rayuwar ta shine abokin rayuwa.
Ta bayyana cewa kuɗi ba matsalar ta bane, sannan a shirye take riƙa bayar da albashi mai tsoka ga duk saurayin da ya yarda ya aure ta.
Budurwar har duƙar da guiwoyin ta tayi ƙasa a cikin ruwan sama tana roƙon samari da su jaraba sa’ar su wajen neman soyayyar ta.
“Daga Cewa Su Gaisa Sai Ta Ƙwace Shi” Budurwa Ta Koka Bayan Ƙawarta Ta Ƙwace Mata Saurayi
A wani labarin na daban kuma, wata budurwa ta koka kan yadda ƙawarta tayi mata ƙwacen saurayi tana ji tana gani.
Wata mata ta koka kan yadda ƙawarta tayi mata ƙwacen saurayi bayan ta haɗa su.
Matar mai suna Munira ta sanya wasu bidiyoyi waɗanda suka nuna irin kusancin dake tsakanin su da ƙawarta wacce tayi mata cin amana.