Daga wakilin Dimukaradiyya Mukhtar Yakubu.
Fitacciyar jaruma a cikin shirin Dadin Kowa Hajiya Zahra’u Sale wacce aka fi sani da Adamar Kamaye. Ta bayyana shirin ta na yin aure, a duk lokacin da ta samu kalar mijin da ta ke so.
Jarumar ta bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da jaridar Dimukaradiyya, a lokacin da mu ke tamabayar ta maganar ko nan gaba tana da niyyar yin aure ganin cewar, shekarun ta sun ja?
Sai ta ce “Ba ni da aure a yanzu, sai dai ina da niyyar yin aure, idan Allah ya kawo mun miji nagari zan yi aure. To Amma ka san su maza har kullum ba sa yi wa matan adalci, wani lokacin kuma matan ne ba sa yi wa mazan adalci, to amma ina son, duk wani mai kauna ta da masoyana, su taya ni da addu’a Allah ya ba ni miji nagari wanda za mu zauna lafiya ni da shi” inji ta
“Ina da niyyar aure, kullum a cikin niyyar nake. Amma dai har yanzu ban dace da kalar wanda zan aura ba, mu zauna da shi din ba ne, sai dai ana nan ana lalube kuma ana bai wa Allah zabi, ya zaba mana abin da ya fi alheri. Dan aure ai ba zai ki yin aure ba” a cewar ta.
Kazalika ta ce,”Don shi aure sunnar Manzon Allah ne, kuma duk Musulmi ba zai ki sunnar Manzon Allah S A W ba. ”
Da muka tambaye ta ko za ta iya auren Kamaye kuwa cewa ta yi “Ai shi Kamaye Ubangidana ne, don haka ina yi masa kallon Ubangidana ne, ba wanda zan aura ba, don ana maganar ko zan aure shi ko Malam Nata’ala, to gaskiya duk a cikin su ban ga miji aure ba. Abokan aiki na ne a harkar fim. ” a cewar Zahra
Daga karshe ta yi fatan alheri ga masoyan ta da su ke nuna mata kauna, domin a cewar ta kaunar da su ke nuna mata ce ta zamar da ita wani abu a duniya.
Comments 1