Masu fafutukan kafa Kasar biafra IPOB sun karyata bayanin wani mai suna Petrus Obi dake cewa, kungiyar na kokarin fara Kai farmakin ga Yan jarida a Yankin Kudu maso Gabashin kasar nan.
Kungiyar ta bayyana cewa, ba ta da wani shiri na kai wa kungiyar yan jarida na Kasa NUJ hare-hare a yankin, face ci gaba da goyon baya, da kuma kare kungiyar ta NUJ a yankin.
Bayanin hakan na kunshene a cikin wata sanarwa da sakataran yada labarai da hulda da kafafen yada labarai na kungiyar IPOB Emma Powerful, inda ya bukaci al’uma su yi watsi da wancan kalaman.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yadda Sanata Uba Sani ya yi taimakon Addinin musulunci
Ya kara da cewa, “Muna son mu bayyana karara cewa, IPOB ba ta da wani mummunan manufa kan kungiyar NUJ, kuma za ta goyi bayan NUJ, tare da kare kungiyar, saboda sun kasance masu fadin gaskiya game da ta’asar da Fulani makiyaya, yan fashi da makami, da kuma yan yan bindiga ke yi a fadin Najeriya.
Kazalika ya ce, “IPOB ba za ta taba iya kai farmaki kan NUJ a Kudu maso Gabashin kasar nan ba, saboda yan jarida ba suba ne matsalar mu ba, a’a abokan aikin su ne” inji shi
A karshe ya ce, “Muna sake jaddada cewa IPOB abokan NUJ ne, kuma ba za su taba daukar wani mataki da zai cutar da su ba” a cewar shi
Comments 1