• Wanda ya yi suna shi Daman ya kamata ya nemi kujerar siyasa.
• Dawayya ta kuma ce tanada sha’awar tsayawa takara a babban zaben shekarar 2023 me zuwa.
• Kuma ja hankalin takwarorin ta Yan fim da su san darajan da Allah ya yi musu.
Rukayya Dawayya.
Daga Mukhtar Yakubu Kano.
Fitacciyar jaruma a masana’antar finafinai ta Kannywood Rukayya Umar Santa, wacce aka fi sani da sunan Rukayya Dawayya, ta soma tunanin ita za ta shiga sahun masu neman wani mukami na siyasa, idan Allah ya kaimu lokacin zabe na shekarar 2023.
Jarumar ta bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin dangane da rawar da ‘yan fim za su taka, a lokacin zabe mai zuwa, inda ta ke cewa “Na shiga siyasa a zaben da ya wuce na yi ta Kano na Jigawa da kuma jihata ta Katsina, domin a nan ma na fi bada karfi a siyasar, don Mahaifina dan Katsina ne, a wani kauye a Matazu, Mahaifiyata ita ce shuwa Arab, amma dai a Kano muke da zama sai dai, duk wasu takarduna na Katsina ne don haka ne, na fi bada karfi a siyasar Katsina “. Inji ta
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnan jihar Cross Rivers ya dakatar da albashin Yan siyasan da basa jam’iyar APC
Ta ci gaba da cewar” kuma Alhamdulillah, yanayin yadda muka gudanar da siyasar ya kara mini karfin gwiwa, kuma na gane cewar, lallai akwai sauran aiki a gaban mu, sabida duk wanda ya ke so ya yi wani yunkuri, wanda zai taimaka wa kansa, to dole ne sai ya zama ko’ina yana nan. Kuma na gane fitaccen mutum, wanda aka sani shi ne ya kamata ya shiga siyasa, saboda abu ne na sanin jama’a, don haka wannan siyasar da na shiga ya sa na samu wani karfin gwiwar da na ke tunanin zan iya fitowa takara idan aka zo lokacin zabe na gaba, kuma ina ji a jikina zan iya cin zaben a duk mukamin da na ne ma. ” A cewar ta.
Daga karshe Rukayya Dawayya ta yi kira ga abokan sana’ar ta da su San darajar da Allah ya yi musu ta farin Jini, kuma su san yadda za su kiyaye mutuncin su, da baiwar da Allah ya yi musu. Dawayya, ta soma tunanin ita za ta shiga sahun masu neman wani mukami na siyasa ne, idan Allah ya kaimu lokacin zabe na shekarar 2023.
Comments 1