Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC ta sanya ranar 12 ga watan Fabarairun 2022 a matsayin ranar da za a gudanar da zaben kananan hukumomi shida da ake da su a birnin Tarayya Abuja, kamar yadda ta saki a cikin jadawalin yadda za a yi zaben.
Mr Festus Okoye, Kwamishinan INEC kan yada labarai da ilmantarwa kan zaben, shi ne ya saki jadawalin a Abuja a ranar Laraba, inda ya ce zaben za a gudanar da shi domin zaben shugabannin kananan hukumomi shida da ake da su a Abuja, da kuma kansiloli 62, wanda wa’adinsu zai kare a watan Mayun 2022.
Ya ce sanya ranar zaben yana daga cikin abin da INEC din ta yanke a zaman da ta yi a ranar Laraba. Okoye ya ce daga cikin abubuwan da aka tattauna ya hada da jadawalin zaben, da kuma ayyukan da za a gudanar wajen gudanar da zaben a Abuja na shugabannin kananan hukumomin da kansiloli wanda INEC za ta shirya.
Ya bayyana cewa za a bude karbar fom mai EC9 (CF001 a da) da kuma EC9B (CF002 a da) domin zaben a ranar 1 ga watan Afrilu. Inda kuma za a gudanar da zaben fidda gwani da kuma magance matsalolin da zai faru daga zaben fidda gwani daga ranar 1 ga watan Afrilu zuwa 24 ga watan na 2021.