Dan wasan gaban Ingila, Harry Kane ya zura wa kasarsa kwallo ta 12 a wasan da kasar Ingila suka lallasa kasar Kosovo a gasar fafatawa domin zuwa gasar Zakarun Turai a 2020. Wasan ya gudana ne a jiya Lahadi, inda Ingila ta samu nasara da ci 4 da 0.
Wadanda suka ci Ingila kwallo sun hada da; Harry Kane, Marcus Rashford da Mason Mount. A halin yanzu Ingila ta kai mataki karshe, inda ta kammala a matsayin na daya a rukunin A da maki 21. Kafatanin wasan wasa daya ne kawai kasar Czech Republic ta doke da su da ci 2 da 1, wanda suma yanzu haka sun yi nasarar zuwa gasar a shekarar 2020 din.
Su ko Kosovo sun kammala a mataki na uku ne da maki 11. Amma za sui ya zuwa gasar idan har suka yi nasarar lashe wasa guda da za a shirya musu.