Aƙall mutum bakwai ne suka ƙone ƙurmus yayin da wasu mutum 18 suka samu raunika daban-daban a wani mummunan haɗarin mota kan babban titin Legas-Ibadan, a ranar Alhamis 13 ga watan Afirilun 2023.
Jaridar Legit.ng ta samo cewa haɗarin motar ya auku ne a wajen gadar Sapaade da ke kan titin a tsakanin wasu motoci biyu, ɗaya ƙirar Toyota Sienna da motas bas ƙirar Mazda.
KU KARANTA KUMA: Yadda wani magidanci ya gano 4 daga cikin ƴaƴan sa 5 ba na shi bane
Direban Sienna ne yake ta sheƙa sauri sannan ya saki hannun sa wanda a cikin hakan ne ya haɗe da motar Mazda ɗin inda nan da nan wuta ta kama.
Kakakin hukumar kiyaye haɗari ta ƙasa (FRSC) ta tabbatar da aukuwar lamarin a birnin Abeokuta na jihar Ogun a ranar Alhamis.
Okpe ta bayyana cewa mutane 27 haɗarin ya ritsa da su, mutum 25 daga ciki maza yayin da sauran biyu babbar mace ɗaya da kuma ƙaramar yarinya, daga cikin mutum bakwai suka rasu yayin da mutum 18 suka samu raunika.
“Jimillar mutum bakwai ne suka ƙone ƙurmus.” A cewar ta
An Yankewa Wani Tela Hukuncin Daurin Shekaru Uku A Gidan Yari
Wata kotun majistare dake jihar Ondo ta yankewa wani tela mai shekaru 41, Tajudeen Olajide, hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari bisa samunsa da laifin cin zarafin wani mutum mai suna Olamiposi Oluwatobi.
Wanda aka yankewa hukuncin da aka samu da aikata laifuka guda daya na cin zarafi ana zarginsa da bugawa Oluwatobi makulli a idon sa.