Sashen jami’an tsaron Farin kaya DSS yace fitaccen jarumin nan Chiwetalu Agu, Rundunar sojin ƙasa ta mika mata shi.
Sashen ya ƙara dacewa, za’a tabbatar an yi mashi adalci.
Mai Magana da yawun DSS Dr Peter Afunaya ya bayyana haka a lokacin wata gajeruwar tattauna da majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya a ranar Juma’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: An kwato Bindigogi da Alburusai daga hannun Yan bindiga a Kaduna
Afunaya yace “sojoji sun kawo mana shi. Kuma za’a yi mashi adalci.”
Amma kuma yaƙi amsa wasu tambayoyi da akayi mashi.
An kama Chiwetalu Agu a Iweke ta Onitsha, jahar Anambra a ranar Alhamis, sakamakon sanya kayayyakin ƴan ƙungiyar rajin kafa ƙasar Biafra da yayi.
Jahar Anambra ta fuskanci rikice-rikice a makonnin da suka gabata, gabanin zaɓen Gwamna a wata mai zuwa.
Hukumomi sun bayyana cewa, haramtacciyar ƙungiyar nan mai neman kafa ƙasar Biafra, ita ke bayan dukkanin Waɗannan hare-hare da aka kai, amma kuma ta musanta hakan.
Agu ya kasance mai goyon bayan gwagwarmayar ƙungiyar Biafra, Kuma ya ƙalubalanci Gwamnatin Nigeria da mai da inyamurai sanuwar ware.
Comments 1