Al’ummar haramtacciyar kasar Isra’ila na dakon sunan sabon Firaminista da Shugaban kasar zai fitar bayan samun tattaunawa da ‘yan siyasa da suka hada da tsohon Shugaban gwamnatin Benjamin Netanyahu da abokin hamayyarsa Benny Gantz.
Shugaban haramtacciyar kasar ta Isra’ila ya dau alkawarin gujewa sake zuwa zabe na uku ganin rashin yardarsa zuwa dan siyasa Benjamin Netanyahu, wanda da zaran ya kasa samun rinjaye a gaba ,zai iya rusa majalisa, sabili da haka shugaban ya dau mataki na shiga tattaunawa da za ta taimaka don samar da gwamnatin hadin gwiwa a Isra’ila.