Firaministan Isra’ila Mista Benjamin Netanyahu ya sanar da aniyar kasarsa ta tsagaita wuta kan hare haren da kasar ke kaiwa kan Falasɗinawa musulmi a Zirin Gaza.
Ya ce yanzu haka majalisar dokokin sa ta amince da bukatar kasar Masar na tsagaita wutar wacce ke rana ta 11 ana yi.
Yanzu haka dai bangarori biyu dake fafatawa cikin wannan yaki wato Hamas da Isra’ila na ci gaba da tattaunawa kan ko yaushe ne ya kamata tsagaita wutar za ta fara aiki, ko da yake rahotanni sun bayyana cewa akwai yiwuwar a daren yau ne komai zai daidaita.
A kalla Falasɗinawa sama da 200 ne suka rasa rayukansu sakamakon luguden wutar na Isra’ila ciki kuma har da yara ƙanana kimanin 65.
Ita kasar Isra’ilan a nata bangare mutane 12 sun riga mu gidan gaskiya cikin har da kananan yara biyu.