‘Yan kungiyar IS da ke yankin Afirka ta yamma sun kashe daya daga cikin ma’aikatan jinkai guda shida na kungiyar Action Against Hunger da aka yi garkuwa da su a watan Yuli.
Dan jarida a Nijeriya, Ahmad Salkida wanda ya san yadda kungiyar ke gudanar da al’amuranta ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter.
Salkida ya ce “an harbi ma’aikacin da bindiga a dab da dab a wani faifan bidiyo” da shi ya samu gani.
Ya kara da cewa kungiyar ta bayar da daililin kashe ma’aikacin ne saboda “gwamnati ta yaudare su” sakamakon watanni da aka kwashe ana tattaunawar sirri tsakanin tawagar masu sasantawa da kuma jami’an gwamnati.
Sai dai kuma Salkidan bai yi bayani ba dangane da yadda ya samu faifan bidiyon ko kuma a wurin da aka kashe wannan mutum ba.
Ahmed Salkida ya kuma wallafa a shafin nasa dai cewa kungiyar IS da ke yankin Afirka ta Yamma wato ISWAP din “ta yi barazanar kashe sauran ma’aikatan na kungiyar Action Against Hunger guda biyar da suka rage.”
Kungiyar ta Action Against Hunger ta tabbatar da batun kisan ma’aikacin na su, a wata sanarwa da kungiyar ta fitar ranar Laraba.
“Mayakan da ke garkuwa da ma’aikacin Action Against Hunger da direbobi guda biyu da ma’aikatan ma’aikatar lafiya guda uku, sun kashe daya daga cikin wadanda suke garkuwar da su”.
A ranar 19 ga watan Yulin 2019 ne dai ‘yan kungiyar suka yi garkuwa da ma’aikatan agajin bayan ‘yan kungiyar sun kai hari kan jerin gwanon motocin ma’aikatan agajin.
Mako guda bayan yin garkuwa da ma’aikatan agajin, sun bayyana a wani faifan bidiyo inda alamu suka nuna lafiyarsu kalau.
A makon da ya gabata rundunar sojin Nijeriya ta rufe ofishin kungiyar Action Against Hunger bisa zargin tallafa wa mayakan Boko Haram da abinci da magunguna.