Rundunar ‘yan sandan Italiya ta cafke wani matashi dan shekara 26 da haihuwa da laifin tuka wata mota kirar Ferrari F430 ta bogi.
Hakan ya faru ne bayan wani farmaki da ‘yan sanda suka kai mai suna ‘Operacion Cavallino’.
KU KARANTA: Zan sayar da dukkan matatun man dake Najeriya
A cewar jaridar The Sun UK, mutumin da ba a san ko wanene ba ya canza wata mota kirar Toyota MR2 Coupe ta zama kamar motar motsa jiki ta Ferrari F430.
A cikin wani faifan bidiyo da ya yi ta yawo a shafukan sada zumunta a ranar Litinin, an ga ‘yan sanda suna raka mutumin a cikin kwafin motar.
An ce motar ta jabu tana da ainihin sassan motar Ferrari da suka hada da gaban motar, murfi na gaba da na baya.
An ba da rahoton tuhumar shi da yin amfani da alamun kasuwanci masu rijista ba tare da izini ba bayan an kai rahoto ga Ofishin Mai gabatar da kara na Jama’a na Asti.
An samar da Ferrari F340 tsakanin 2004 zuwa 2009 kuma kudin ta ya kai £180,000, fiye da kudin da akan siyi MR2.
Wani mai magana da yawun Hukumar Tsaron Italiya di Fianza ya ce a cikin wata sanarwa: “Ayyukan ‘yan sanda na cikin hadin gwiwa da mai gabatar da kara na Asti.” “Muna kokarin abun da kasar mu ta samar mu kare shi, wajen ganin cewa bata gari basu lalata mana shi ba.”
A wani labarin kuma: Kasashen G7 Sun Dauki Wani Mummunan Mataki Kan Rasha
Farsashin ɗanyen mai ya tashi a kasuwannin duniya , bayan manyan masu fitar da ɗanye mai sun amince su ci gaba da rage yawan man da suke fitarwa , yayin da ƙungiyar ƙasashe 7 masu ƙarfi tattalin arziki wato G7 da ƙawayensu su kace zasu rage farashin manfetur ɗin ƙasar Rasha.
Farashin ɗanyen mai ya ƙaru da kashi 0.6 inda a yau Litinin da safe farashin Ganga ɗaya ya kai Dalar Amurka 86.