Jagoran yan adawa a kasar Rasha Alexei Navalny ya sanar da janye yajin cin abinci da yake yi bayan shafe kwanaki ashirin da huɗu ba tare da ya kurbi ko da ruwa ba a gidan yari.
Navalny ya dauki wannan mataki ne yan sa’o’i bayan da likitocin shi suka shawarce shi da ya nemi wani abin tabawa don ceto rayuwar shi.
A ranar talatin ga watan Maris ne dai Mista Navalny ya sanar da fara yajin cin abinci tare da kuma da mika bukatar ci gaba da bashi kulawar lafiya.
Cikin wani sako da ya wallafa a shafin sa na Instagram, Jagoran yan adawar ya ce likitocin nashi sun gargade shi da cewa muddin fah bai nemi wani dan abu ya sanya a bakin salati ba to yana iya bankwana da duniya sakamakon yunwa.
An garkame Mista Navalny ne wanda ya yi kaurin suna wajen sukar gwamnatin shugaba Vladmir Putin bayan dawowa daga birnin Berlin na kasar Jamus sakamakon matsala da ya samu a lakar shi a wani harin watan Janairu.
Mahukunta a kasar ta Rasha sun nesanta kan su da wannan hari, to sai dai a watan Disambar bara ne Navalny ya wani shagube wa Jam’ian FSB na kasar inda ya ce suna son ganin bayansa.