Tawagar hadin gwiwa ta ‘yan banga da mafarauta, a ranar Lahadin da ta gabata, ta yi nasarar dakile garkuwa da wasu matafiya a gadar Ahoko, da ke kan hanyar Abuja zuwa Lokoja.
Wani mamban ‘yan banga, wanda ke cikin aikin hadin gwiwar, amma ya gwammace a sakaya sunansa, ya ce an kama mutanen biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne.
Ya ce, kwatsam masu garkuwar sun bayyana a wata kwana da ke da nisa da gadar, kuma suna shirin budewa motocin wuta ne a lokacin da tawagar ‘yan banga da mafarauta suka isa wurin.
“A gaskiya muna cikin sintiri tare da ‘yan banga da mafarauta a yayin da muke gangarowa kan gadar, sai ga wasu biyu daga cikin masu garkuwa da mutane sun fito kwatsam suka yi yunkurin bude wuta kan wata mota, inda nan take muka kama su.” Inji shi.
Ya ce masu garkuwa da mutanen biyu sun yi yunkurin tserewa ne, bayan da bindigoginsu suka ki tashi domin yin harbi, amma nan take aka kama su.
“Amma sauran ‘yan kungiyar da ke boye a cikin daji kusa da bakin titi nan take suka tsere bayan da suka gano cewa an kama mambobinsu biyu,” inji shi.
Dan bangan ya ce an mika masu garkuwa da mutanen biyu ga jami’an tsaro a Lokoja, babban birnin jihar Kogi tare da bindigogi biyu da aka kwato daga hannunsu.
Ya ce rundunar ta yi ta yin sintiri cikin dajin da ke kewayen yankin domin gano maboyar Yan bindigan.
Kwamandan kungiyar mafarautan na jihar Kogi, Hassan Yakubu, ya tabbatar da kama wasu mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a Ahoko, inda ya ce an mika wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne ga jami’an tsaro.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, CSP Williams Ovye Aya, har yanzu bai samu amsa kiran waya ko amsa sakon da aka aike wa layin wayarsa ba, kan lamarin.