Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta ce ta ceto jarirai uku tare da kama wasu mutane 16 da ake zargi da laifin safarar yara da hada baki wajen sata.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, PPRO, ASP Mahid Abubakar, ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a madadin kwamishinan ‘yan sanda, Haatu Usman, a Gombe ranar Laraba.
Karanta nanGobe Juma’a Kotun Koli Zata Yanke Hukunci Akan Shari’ar Abba Da Gawuna
Abubakar ya ce an samu nasarar ne a karshen mako biyo bayan rahoton sirri da aka samu daga al’ummar Barunde na jihar Gombe.
Ya ce an ceto jarirai uku daga hannun wadanda ake zargin a cikin jihar, yayin da wasu biyu kuma aka yi safarar su daga jihar.
A cewarsa, daya daga cikin jariran da aka yi safararsu a yanzu yana Legas, yayin da dayan kuma an sameshi a Anambra,ya kuma bayyana cewa ana kokarin kwato sauran jariran biyu da kuma mayar da su jihar.
Abubakar ya bayyana cewa, yayin bincike, an gano cewa an sayar da daya daga cikin jariran kan Naira 400,000.
Ya ce an sayar da yaron ga wani mai saye a jihar tare da hadin gwiwar wani ma’aikacin jin dadin jama’a a jihar.
Ya ce wadanda ake zargin sun kafa wata masana’antar jarirai inda aka ajiye wadanda suka haihuwar a wani wuri kuma ana sayar da jariransu bayan an haife su.
A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan, rundunar ta samu rahoton sirri kan daya daga cikin iyayen da suka sayar da danta ga wadanda ake zargin.
A wani labarin kumaWata Sabuwa: Ƙungiyar Ƙwadago ta bayar da wa’adin kwanaki 14 ga gwamnati
Wannan wani laifi ne na hada baki da fataucin yara inda aka kama wata Khadija Manzo da wasu 15 bayan wani rahoton sirri da aka samu daga al’ummar Barunde a karshen mako.
A wani lokaci a shekarar da ta gabata, wata Khadija Manzo da wasu 15 sun shiga harkar sayar da jarirai ga mabukata.
Da samun rahoton, jami’an tsaro na Lowcost Division sun gudanar da bincike wanda ya kai ga kama Manzo, da sauran wadanda ake zargi,” in ji shi.