Jami’an Tawagar Yan sanda na jihar Niger dake yaki da Masu tada kayar baya, sun kashe hamshakin mai bai wa yan bindiga bayanan sirri Mai suna Buba Baromi, tare da wasu mabiyan shi 3, ya yin wani musayan wuta da ya afku tsakanin bangarorin biyu a garin Dogon Fadama na karamar hukumar Kontagora dake jihar.
Rahotannin da Jaridar Dimokuradiyya ke samu na nuna cewa, an kashe Baromi ne a maboyarvshi dake dajin Damba dake jihar.
Jami’an yan sandan sun kashe Baromi ne lokacin da yake tare da Mabiyasa a wani musayan wuta, da ya yi sanadiyar raunata wasu daga cikin yan bindigan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Kaduna ta haramta saffarar dabbobi a jihar
Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa, tawagar jami’an yan sandan dake yaki da masu tada kayar baya, sun farmaki maboyar Baromi ne karkashin jagorancin wani Mafarauci wanda jami’in sakai ne.
Wata majiya ta bayyana wa manema labarai cewa, An kashe Baromi ne a rana ta biyu da jami’an suka kai farmaki, ya yin da sauran mambobin shi aka kashe su tun a farmakin farko da rundunar yan sandan ta kai.
Majiyar ta kuma bayyana cewa, Baromi ba bayanai kadai ke bai wa yan bindiga ba, inda ya kan jagoranci su zuwa Kai hari ko garkuwa da mutane a wasu yankunan na jihar Niger.
” Shine ya jagoranci satar Shanu, da kuma Kai harin garin Dogon Fadama a watan da ya gabata, wanda harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama wadanda basuji ba basu gani ba” inji majiyar
Sai dai duk yunkurin da mane ma labarai suka yi, domin ji ta bakin jami’in Hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar DSP Wasiu Abiodun, a bun ya citura.