Wata gidauniyar aikin noma ‘Agro-processing, Productivity Enhancement, and Livelihood Support (APPEALS)’ tare da hadin gwiwar cibiyar binicike da bunkasa harkar noma ta ‘Institute of Agricultural Research (IAR)’ dake jami’ar Ahmadu Bello Zariya, sun samar da ingatacciyar irin shinkafa kala 4 ga namoman jihar Kano.
Shugban gidauniyar APPEALS a jihar, Alhaji Hassan Ibrahim, ya bayyana haka yau Asabar a gangamin gabatar da irin da aka yi a garin Kadawa dake karamar hukumar Garun Malam a jihar.
Ibrahim ya kuma kara da cewa, an samar da irin shinkafar ne kala 4 don manoma su samu girbi mai yawa ta hanyar kashe kudade kadan.
Ya kuma ce, babu manomin da zai samu cikakken nasara in har bai samu irin daya dace ba da kuma yin feshin maganin kwari da suka dace, haka kuma in har an samu iri mai kyau basai an sha wahala ba wajen yn feshi na tsawon lokaci.
“Wannan ganganim sakamako bincike ne da muka yi na hadin gwiwwa, muna kuma sam cikakken nasara a gwajin irin da aka yi, akan haka muka ga ya dace a gabatar wad a manoma inganatccen irin do suma su ci gajiyarsa.
Ya kuma kara da cewa, wadanda za su amfana da irin za su samu jari daga kamfanin don su cigaba da harkar noma shinkafa da kuma sauran albarkatun gona kamar su tumatur da alkama da saurasu ta haka ne za su samu cikakken amfanin yadda ya kamata.
Ya ce, tuni aka yi nisa don taimaka wa masu chasar shinkafa na Kwanar Dawaki don su samar da shinkafa tamkar shinkafar gwamnati.
Shugagan tashar IAR na Kadawa, ya cewa, sabon irin zai taimaka wa manoma samun girbi mai yawa a karshen damuna.
”In har manoma za su yi amfani da sabon irin lallai girbinsu zai karu sosai,” inji shi.
Ya kuma ce sabbin irin sun hada da WITA 4 da FARO 60 da FARO 66 da kuma FARO 57.
A jawabinsa a mamadin manoman jihar, Sarkin Noman Kano, Alhaji Yusuf Nadabo, wansa Malam Abdulrahman Yusuf ya wakilta ya yaba wa APPEALS da kuma IAR da suka samar wa al’umma sabon irin shinkafa.
Ya kuma ce, manoman yankin Kadawa sun yi amfani da irin sun kuma ga amfaninsa a kan haka kuma za su ci gaba da amfani a irin don samun cigaba a sana’arsu, ya kuma buqaci manoma su yi ragista da APPEALS don su samu amfani irin yadda ya kamata.