Rahotanni daga Zariya na cewa; Jami’ar ABU ta sanya hannu akan wata yarjejeniyar fahimtar juna da wasu jami’o’in kasashen ketare guda biyu a wani mataki inganta harkar ilimi a jami’ar.
Shugaban cibiyar koyar da Harkokin shari’ar Musulunci, CILS, Farfesa Muhammad-Bello Uthman ne ya bayyana haka a yayin taron alkalai karo na 21 da aka yi a garin Zariya ranar Lahadi.
Uthman ya bayyana cewa, jami’oin sun hada da ‘Al-Azhar University Cairo, Egypt’ da kuma ‘International University of Africa, Khartoum, Sudan.