By Ishaq Dabai
Majalisar gudanarwar jami’ar Ahmadu Bello ABU dake Zaria, ta amince da nadin Malam Rabi’u Samaila a matsayin babban magatakardar cibiyar da kuma Malam Mohammed-Bello Gurin a matsayin sabon bursar.
Malam Auwal Umar, wanda shine Daraktan Hulda da Jama’a na jami’ar, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai ranar Juma’a a Zariya.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya rawaito cewa wa’adin tsohon magatakarda, Abdullahi Kundila, ya kare tun a ranar 2 ga Yuni.
Sanarwar ta ce nadin manyan jami’an guda biyu ya samu amincewar kwamitin hadin gwiwa na Majalisar Dattawa a taron da ya gudana a ranar 17 ga Satumba, “Duk nade naden za su fara aiki nan take, Kowannen su zai yi hidimar wa’adi daya na shekaru biyar.
Sanarwar taci gaba da cewa sai da aka samu “Amincewar Majalisar game da nade naden na cikin ikon da Sashe na 6 (1) na Jami’oi na Dokoki daban daban wanda aka Kwaskware Dokar a shekarar 1993, kamar yadda aka gyara,” in ji sanarwar.
Kafin nadin nasa, Umar ya kasance mataimakin magatakarda, a sashin bunkasa ma’aikata, sannan kafin haka sabon magatakardar ya yi aiki a matsayin mukaddashin magatakarda kuma sakataren majalisar jami’ar sau biyu, tsakanin watan Disambar 2014 zuwa Satumba 2015 da tsakanin watan Fabrairu zuwa Yuni na 2016.
Kazalika, sanarwar ta ce Gurin, sabon bursar da aka nada, shi ne Bursar na Jami’ar Tarayya, Gashua.Ya kasance a matsayi na biyu daga ABU, baya da haka Gurin ya fara aiki a matsayin mataimaki babban jami’in kula da malamai (Accounts) a ABU a ranar 6 ga Yuni, 1988, sannan ya hau kan mukamin ya zama Mataimakin Bursar.