Babban jam’iyar adawa a kasar Sudan ta Kudu ta janye daga zaman Kwamitin Samar da zaman lafiya a kasar inda ta zargi dayan bangaren da Kai wasu hare-hare na babu gaira babu da dalili.
Jam’iyar adawar ta Sudan People’s Liberation Movement ta zargi cewa dayan bangaren da cewa, ya kai wani sabon hari a ranar Litinin.
Mataimakin Shugaban kasa Riek Machar ne ke jagoratar jam’iyar, Wanda ya kafa gwamnatin hadaka da tsohon abokin hamaiyarsa Salva Kiir shekaru biyu da suka gabata.
Sai dai ci gaba da takun sakar da ake samu tsakanin mutanen biyu ya hana aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da nufin kawo karshen yakin basasar da aka shafe shekaru biyar ana yi a kasar, inda mutane sama da dubu Dari hudu suka rasa rayukansu sanadiyar yakin.
A wani labarin Kuma na daban.
NNPP ta samu Sabbin Shuwagabanni a Nasarawa, tasha alwashin ƙwace Kujerar Gwamna Sule a 2023
Jam’iyyar Mai Alamar Kayan Marmari NNPP ta ƙaddamar da sabbin shugabannin ta a Jahar Nasarawa, wanda zasu jagoran ci harkokin Jam’iyyar zuwa Shekaru huɗu.
Jam’iyyar, a lokacin da take ƙaddamar da shugabannin ta da suka samu nasara ta hanyar sasanci daga faɗin Ƙananan Hukumomi 13 na Jahar a lokacin zaɓen ta, tasha alwashin ƙwace Kujerar Gwamnan Jahar Nasarawa a Shekarar 2023.
Dayake jawabi a Lafia a ranar Talata, Sabon Shugaban Jam’iyyar Sidi Bako yace Jam’iyyar NNPP tana buƙatar shugabanci mai kyau domin ta kawo romon Dimokuraɗiyya ga Mazauna Jahar.
Yace “Jam’iyyar NNPP nada shugabanni masu ƙarfi a faɗin Ƙananan Hukumomi 13 na Jahar, kuma ina farin cikin sanar daku cewa Jam’iyyar mu zata samu nasara a Babban Zaɓen Shekarar 2023, domin mazauna garin su kurɓi romon Dimokuraɗiyya
” Bama goyon bayan Siyasar Uban gida da kuma ƙaƙaba Ɗan takara, wanda Al’umma basa so. Wannan jam’iyya zata baiwa mutane dama su zaɓi Shuwagabannin su da kan su.
“Jam’iyyar nada Mataimakan Shugaban Jam’iyya guda uku a faɗin shiyyoyi uku, da kuma sauran jami’ai Da suke a shirye domin cigaban Jam’iyyar. Da yardar Allah, zamu karbi ragamar Shugabanci a Shekarar 2023.”
Tunda Farko, Sakataren Jam’iyyar na yankin Arewa ta Tsakiya Umar Auta yace Jam’iyyar nada manufar samar da kyakkyawan Shugabanci a Jahar dama Ƙasa baki ɗaya.
Rahotanni sun nuna wasu daga cikin waɗanda aka zaɓa akwai Thomas Luka, Sakatare Ladan Ɗanlami, Ma’aji Nasir Mariga, odita-Janar, da sauran su.