Kasar Poland ta dauki matakin fatattakar mambobin difulomasiyya na kasar Rasha guda 45, bisa zargin su da yiwa ƙasar leken asiiri, kamar yadda Kakakin Ma’aikatar kula da harkokin wajen kasar ya bayyana.
Kana Kakakin kasar Poland kan ayyukan na musamman Stanislaw Zaryn ya bayyana cewa, Ana Zargin Yan kasar Rashan ne da kasancewa jami’an leken asirin Rasha ko kuma masu aiki da jami’an.
Mr Zaryn ya ce, an gano daya daga cikin Mabobin difulomasiyyan ne lokacin da yake binciken wani dan kasar dake aiki a Ofishin adana bayanan al’umar kasar na Warsaw.
Sai dai da sanyin safiyar yau Laraba Jakadan Rasha a Poland Sergey Andreyev da ya ziyarci Ofishin Ma’aikatar harkokin waje na Poland ya karyata zarge-zargen da akewa Yan kasar nasa.
A wani labarin Kuma na daban.
Gobara ta kama a Gadar Lagos, ta laƙume Shaguna da dama
Shaguna da dama a wajen Gadar Apgbo dake Ebute Ero ta Lagos sun ƙone ƙurmus, bayan Gobara ta tashi a Gada da sanyin safiyar ranar Laraba.
Gobarar, wanda ta fara da misalin ƙarfe 1, ta kawo cunkoso a wajen, kuma ta shafi Harkokin Kasuwanci, a yayinda Jami’ai ke ƙoƙari domin magance ta.
Ofishin Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasa dake Lagos Ibrahim Farinloye yace Ma’aikatar Ayyuka ana kira data kulle hanyar, tare da gudanar da bincike, domin gano lafiyar gadar domin cigaba da amfani da’ita.
Yace “Shaguna da dama sun ƙone. Wurin da lamarin ya faru shine Ebutte Ero. Shagunan da suka ƙone yawancin su Kayayyakin Haɗa Biredi da cin cin.
NEMA ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 6:00, an kuma turo Ma’aikatan Hukumomi Kashe Gobara na Ƙasa dana Jaha. Kuma har yanzu ba’a san abunda ya haddasa Gobarar ba.”
Farinloye ya buƙaci masu Motoci dasu yi amfani da wata hanyar.
Yace “zirga-zirga daga hanyar Ikorodu, suyi amfani da Jibowu zuwa Yaba da Onyingbo, daganan zuwa Adeniji zuwa Ebutte Ero ko kuma su cigaba zuwa hanyar Marina.