Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa jam’iyyun APC da PDP jam’iyyu ne matattu, yayin da NNPP ita ce mafi inganci da sahihanci a 2023.
“Jam’iyyar NNPP ita ce babban mafarkin jam’iyyun APC da PDP a zabukan dake tafe a 2023 kuma mafi inganci da sahihanci a madadin APC da PDP wadanda suka gaza a kasar nan tsawon shekaru,” inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hotuna: Yadda Kwankwaso Ya Tarbi Tsohon Na Hannun Daman Ganduje
Da yake jawabi yayin wata tattaunawa da kungiyar Kiristoci ta Najeriya CAN na jihohin Arewa 19 da kuma reshen babban birnin tarayya Abuja a karshen mako a Kaduna, Kwankwaso ya ce jam’iyyar APC mai mulki ta addabi kasar nan da talauci da cututtuka, wanda abin takaici ne.
“APC ta tabbatar ta fi PDP muni, jam’iyyu matattu ne, kuma idan wani yana tunanin za su canja da kyau, irin wannan mutumin yana yaudarar kansa ne ko kuma ya zama mai barna”.
“A zabe mai zuwa, kada kuri’a ta kasance bisa ra’ayi na zabin wanda zai zama shugaban kasa. A matsayina na musulmi na goyi bayan tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da Goodluck Ebele Jonathan wadanda kiristoci ne kuma sun zama shugabannin kasa a kan Buhari.”
“Idan akwai wanda ya fi ni takara, zan mara masa baya domin amfanin kasa. Idan ‘yan Najeriya za su sake yin kuskure wajen zaben shugabanni a 2023, bai kamata mu zargi kanmu ba kuma ba kowa.”
“Na yi takara sau 18, na yi nasara sau 15, na kuma yi rashin nasara sau 3. Na koyi abubuwa da yawa game da yadda ake tafiyar da kasawa da nasara. Na biya kudina a siyasance tsawon shekaru kuma na fahimci yadda zan tafiyar da kalubalen Najeriya, na yi imanin cewa na shirya tsaf don mulkin Najeriya.”
“Tare da al’amurana na siyasa da tafiyar da al’amuranmu daban-daban kamar yadda na nuna a matsayina na gwamnan jihar Kano ba tare da la’akari da addini ko kabila ba, zan iya yin irinsa a Najeriya idan aka ba ni dama a 2023 a matsayin shugaban kasa.”
“Ni na kowa ne domin a matsayinka na shugaba dole ne ka kasance mai gaskiya da adalci.”
Kwankwaso ya ce, idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa, zai gyara gine-ginen tsaro tare da kara jami’an tsaro don magance matsalolin tsaro da ke addabar Najeriya.
“Zan baiwa ilimi da samar da aikin yi fifiko, in fito da tsare-tsare da za su bunkasa tattalin arzikin kasa…” Inji shi.
A wani labarin kuma,Yan Majalisar Wakilai Sun Raina Kason Da Aka Ware Musu A Kasafin 2023
Majalisar wakilai ta tarayya ta koka kan yadda kasafin kudin majalisar ya gaza.
Kakakin Majalisar Wakilan, Benjamin Kalu, ya ce Majalisar ba za ta iya yin aiki yadda ya kamata ba, idan har za a tafi a wannan kasafin kudin da aka ware mata.