Allah Ya yi wa Jarman Kano Farfesa Isa Hasim rasuwa. Ya rasu ne a ranar Lahadi yana da shekara 86 kamar yadda wani surukinsa ya tabbatar wa BBC.
Babu dai wani cikakken bayani kan dalilin rasuwarsa.
Amma rasuwarsa na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 da rasuwar Sarkin Rano Alhaji Tafida Abubakar Ila wanda Allah Ya karbi ransa a ranar Asabar.