Jarumin fina-finan Hausa na Kannywood wato Bello Muhammad Bello (BMB) ya cikar alkwarin da ya dauka na aske kansa mutukar Shugaban kasa Buhari ya lashe zaben 2019.
A makon data gabata ne BMB ya saki hotunansa a kafar sadarwar zamani ta Instagram kansa babu gashi ko daya,inda yayi kansa kwal kwabo, bayan kwashe tsawon shekara 10 yana tara gashin. Kuma yayi haka ne don cika alkawarin daya dauka na cewa mutukar Buhari yaci zaben 2019 zaiyi hakan.
“Wani furodusa ya taba min tayin naira miliyan 1.5 domin na aske gashin kaina na fito a wani shirin fim dinsa, amma kememe na ki, amma a yanzu a shirye nake na aske gashin saboda farin cikin samun nasarar Buhari, wannan zai nuna irin soyayyar da nake yi ma Buhari.” Inji shi.
Jarumin ya aske gashin nasa ne a ranar Juma’a, wanda ta yi daidai da ranar haihuwarsa.
Da fatan suma shugaban nin zasu dinga cika Nasu alkawuran duba da yanda mutane suke nuna musu kaunar da takai suna iya aikata wasu abubuwa dan nuna soyayya akan su.