A ƙarshen makonnan ne dai hukumar ƙaallon ƙwallon ƙafa ta nahiyar Afrika wato CAF haɗin gwiwa da hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya wato FIFA ta fitar da jerin ƙasashen da sukafi iya taka leda a nahiyar Afrika daga ta 1 zuwa ta 10.
Sai dai za a iya cewa abin bai yiwa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles daɗi ba duba da yadda ta sami koma baya a nahiyar Afrika dama kuma tsaiwar jaddawalin da aka fitar na duniya inda daga magaki na 3 a nahiyar Afrika ta dawo mataki na 4.
Ga jerin yadda aka fitar da jaddawalin tsaiwar ƙasashen:
1. Senegal.
2. Tunisia.
3. Algeria.
4. Nigeria.
5. Morocco.
6. Ghana.
7. Egypt.
8. Cameroon.
9. Mali.
10. Burkina Faso.
A yanzu dai a tsaiwar jaddawalin da aka fitar na duniya Najeriya ta koma matsayi na 32 inda da take a matsayi na 29 a duniya. Yanzu ta sake samun gagarumin koma baya.