Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta wanke Barcelona a wasan mako na bakwai na gasar Laliga ta ƙasar Andalus da suka fafata a wannan yammaci na Asabar a filin wasa na Camp Nou dake birnin Catalonia na ƙasar Andalus.
Ta sami nasara ne daci 2 da 1 inda Federico Valverde ne ya fara jefa ƙwallo a dai-dai mintina na 5 sanan kuma Ansu Fati ya rama ƙwallon a dai dai mintina na 8. Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne Sergio Ramos ya jefa ƙwallo ta 3 a dai-dai mintina na 63 ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaron gida. Gab da za a tashi wato a mintina na 90 Luca Modric ya sake jefa ƙwallo ta 3.
Ayanzu ta tabbata cewar Real Madrid ta sami maki 3 a filin wasa na Camp Nou kuma tana da maki 13 a tsaiwar teburin gasar ta Laliga biyo bayan wasan mako ba 7 da aka fafata. Saidai za a iya cewa Real Madrid nada kwantan wasa guda ɗaya yayin da Barcelona take da kwantayen wasanni guda 2.
Wannan itace haɗuwa ta farko tsakanin mai horas wa Zinedine Yazid Zidane da Roland Koeman, shidai Koeman sabon mai horas wane na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona da suka kori Setien suka kawoshi a kakar wasa ta bana.