An fara fafata gasar zakarun nahiyar turai a shekarar 1956, amma ita kanta gasar an ƙirƙireta a shekarar 1955 wato shekaru 65 kenan da suka gabata, amma ba a fara bugata ba sai a shekarar 1956 inda aka sami ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa daga ƙasashen turai daban-daban da suka fara fafata gasar a karon farko.
A kakar wasan dai an sami jerin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa har guda 16 da suka fafata gasar kuma kowacce ƙungiyar ƙwallon ƙafa a cikinsu akwai irin bajintar da tayi kuma da irin gudun mawar data bayar kuma wasan an gudanar dashi yadda ya kamata duk da cewar farkon fafata gasar ne.
Ga jerin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan da suka fara fafata gasar ta zakarun nahiyar turai:
1. Voros Lobogo na ƙasar Hungry.
2. A.C Milan na ƙasar Italiya.
3. Stade de Reimes na ƙasar Faransa.
4. Sporting CP na ƙasar Portugal.
5. Real Madrid na ƙasar Andalus.
6. AGF Aarhus na Denmark.
7. Anderletcht na ƙasar Belgium.
8. Djurgarden na ƙasar Sweden.
9. Gwardia Warszawa na ƙasar Poland.
10. Hibernian na ƙasar Scotland.
11. Partizan na ƙasar Yugoslavia.
12. PSV Eindhoven na ƙasar Netherlands.
13. Saarbrucken Saar na ƙasar Switzerland.
14. Servette na ƙasar Switzerland.
15. Rot-Weis Essen na ƙasar yammacin Jamus awancan lokacin.
16. Rapid Wein na ƙasar Austria.
Waɗannan jerin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan guda 16 sune suka fara fafata gasar zakarun nahiyar turai a shekarar 1956, sai dai wani abin mamaki shine a halin yanzu duk wasu ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan babu su inda za a iya cewa a jerin ƙungiyoyin da zasu fafata gasar zakarun nahiyar turai daza’a fara a yau Talata za a iya cewa daga jerin ƙungiyoyinnan guda 16 da suka fara buga gasar Real Madrid ce kawai ta rage wadda zata fafata wasan gasar ta bana.
Haka zalika a shekarar da aka fara fafata wannan gasa ta zakarun nahiyar turai ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ce ta lashe gasar bayan data doke ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Stede de Reims na ƙasar Faransa daci 4 da 3 a wasan ƙarshe da suka fafata a filin wasa na Parc des Princes dake ƙasar ta Faransa.