Hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC) ta gargaɗi mutane akan siye da amfani da wayoyin hannu waɗanda ba a amince da su ba.
Hakanan kuma hukumar ta sanar da tara mai tsauri akan ƴan kasuwan dake sayar da gurɓatattun wayoyi ga ƴan Najeriya. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA: Yadda wata matar aure ta mayar da mijinta shalele ya ɗauki hankula
Hukumar NCC ta bayyana hakan ne bayan jami’an ta sun cafke wani Yahaya Ado na kamfanin Gezawa bisa sayar da wayoyin bogi ƙirar Gionee.
A cikin sanarwar ta hukumar NCC, tayi gargaɗin cewa wayoyin da ba a amince da su ba suna da janyo wa masu amfani da su asara sannan ga rashin biyan buƙata.
Ga jerin sunayen wayoyin da ba a amince da su ba a Najeriya:
- Wayoyin Gionee ƙirar G800 da L990.
- Wayoyin H-Mobile ƙirar it5606+ da H351.
- Wayoyin FoxKong ƙirar F30, da F300.
- Wayoyin KGTEL ƙirar K2160 da KG1100.
Haka kuma shafin yanar gizo na hukumar NCC ya fitar da jerin wayoyi 1,891 na kamfanunnika da dama da aka amince da su.
Jerin ya ƙunshi wayoyin Nokia, Apple, Fero, Motorola, Huawei, Sony Ericsson, Itel, LG Samsung, da dai sauran su.
Shugaba Buhari Ya Yi Alkawarin Tallafawa Wata Kasa Da Man Fetur Duk Da Karancinsa a Najeriya
A wani labarin na daban kuma, shugaba Buhari yayi alƙawarin tallafawa wata ƙasa da man fetur duk ƙarancin sa da ake fama da shi a Najeriya.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce kasar za ta tallafawa Jamhuriyar Burundi kan matsalar karancin man fetur don nuna hadin kai da ‘yan uwantaka a Afirka.
A cewar Femi Adesina, mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Buhari ya bada wannan tabbacin ne a ranar Talata 3 ga watan Janairu a fadar shugaban kasa dake Abuja, yayin da yake karbar bakoncin manzon musamman na shugaban kasar Burundi Evariste Ndayishimiye wanda ya zo da sako