Ta gabbata manyan ‘yan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles guda uku kuma jiga-jigai bazasu sami damar buga wasannin da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles zata fafata na sada zumunci ba a wannan makon da ƙasashe suke yunƙurin buga wasannin sada zumunci yayin da wasu kuma sukeyin yunƙurin buga wasannin share fage na neman cancantar buga kofin nahiyarsu.
Manyan ‘yan wasan da bazasu sami damar bugawa Super Eagles wasa ba guda uku dukkaninsu suna cikin mutane 11 na farko da ake fitowa dasu domin fafata wasa, guda biyu daga cikinsu ‘yan wasan tsakiya ne yayin da guda daga cikinsu mai zura ƙwallo ne a raga kuma ya shahara sosai wanda rashinsa na ganin kamar akwai barazana a ɓangaren ‘yan wasan gaban na Super Eagles.
Haka zalika suma ragowar ‘yan wasan na tsakiya guda biyu da bazasu sami damar buga wasanba ana ta tararrabin suwaye za a sanya domin su maye guraben nasu a wasannin sada zumuntar guda biyu da ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Super Eagles zata fafata duba da cewar ta kwashe watanni ba tare data buga wasan sada zumunci ba kokuma wata gasa.
‘Yan wasan da bazasu sami damar buga wasannin ba sune akwai Oghanekaro Etebo wanda yake buga wasansa a wata ƙungiyar ƙwallon ƙafa dake ƙasar Turkey, sannan kuma akwai Wilfred Ndidi wanda yake buga wasansa a gasar ajin Furimiya ta Ingila a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Leicester City dake ƙasar Ingila. Haka zalika shima shahararren ɗanwasan nan wanda yafi kowa tsada a nahiyar Afrika wato Victor Osinhem bazai sami damar buga wasansa.
Sai dai shi Oghanekaro Etebo da Wilfred Ndidi dukkaninsu rauni ne dasu yayin da shikuma Victor Osinhem duba da yadda akayiwa ‘yan wasan Napoli gwajin cutar Coronavirus inda hakanne ma yasa Napoli bata buga wasanta na mako na uku ba da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus a ƙarshen makon da ya gabata yasa ita Napoli ta roƙi alfarmar basai ya buga wasansa.
Najeriya dai zata fara fafata wasan farko da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙaar Algeria a ranar Juma’a inda kuma zata fafata wasa na biyu da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Tunisia a ranar Talata, za a fafata dukkanin wasannin guda biyu a can nahiyar turai wato a ƙasar Austria.