Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ya bayyana cewa jirgin dakon kaya na Najeriya da ake jira zai tashi nan da watan Afrilun shekarar 2022 mai kamawa.
Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida a gidan gwamnatin tarayya a ranar Laraba bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya na mako-mako da ake gudanarwa.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya jagoranci taron a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito Mista Sirika na cewa kamfanin dakon kaya na kasa zai kasance karkashin wani kamfani wanda gwamnati za ta mallaki kashi 5% a cikinsa.
Ya kara da cewa, ‘yan kasuwan Najeriya za su rike kashi 46%, yayin da sauran kashi 49% za a kebe su har yanzu ba a sanya su ga abokan huldar kasuwanci ba, ko da masu zuba jari na kasashen waje.
Ya kuma kara da cewa kamfanin na kasa idan ya fara aiki, zai samar da ayyuka kusan 70,000 ga ‘yan Najeriya.