Majalisar Wakilai ta umurci kwamitinta kan harkokin tsaron kasa da ya yi wa majalisar bayani duk matakan da ake dauka na inganta harkokin tsaro a kasar.
Kudurin ya biyo bayan wani kudiri na gaggawa kan batun sace wasu mutane tare da kashe daya, a hanyar Kaduna zuwa Abuja ranar Lahadi.
‘Yan majalisar sun koka kan abun da suka bayyana da tabarbarewar yanayin rashin tsaro duk da makudan kudade da ake warewa fannin na tsaro.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda suka kashe wani jigon jam’iyyar APC, Sagir Hamidu.
Hamidu wanda tsohon Daraktan Protocol ne a babban birnin tarayya Abuja, kwanan nan ya tsaya takarar kujerar gwamna a jihar Zamfara kuma an ce ya zuba ido a kan kujerar a zaben 2023 mai zuwa.
Rahotanni sun ce harsashin bindigar ‘yan bindigar da suka yi ta harbe-harbe a kai a kai ya raunata shi wanda ya yi sanadinsa har lahira, inda wasu da dama suka jikkata.
Shaidu sun ce ‘yan bindigar sun kuma yi awon gaba da matafiya da dama tare da kwashe wasu kayayyaki masu daraja.