Wani Mashahurin Mai Nazarin Siyasa a Najeriya, Alh. Bala Usman, ya ce Jihar Kano ba ta Taba yin Gwamna mai Son Cigabanta Irin Ganduje ba, Duba da Yadda ya zo ya Samu Masarautar Kano a cushe waje Daya Amma ya Fadada ta Zuwa Gida Biyar a Maimakon yadda ta ke a da.
Usman ya Fadi Haka ne a yayin Zantawar sa da Wakilinmu Mu’azzam Yakubu Sanka, inda ya Kara da cewa da Mutane sun Fahimci Hikimar Gwamna na yin wannan Abin Alheri ga Kanawa Lallai da Kamata yayi Muyi Masa San Barka Sabanin Suratakan da wasunmu ke yi.
Kazalika ya ce Hatta ma ‘yan Adawa sun Fahimci Dimbin Alherin da ke Tattare da Karin Wadannan Masarautu amma Gilli ya hanasu su Nuna ma Jama’a madadin su kame Bakin su Sai Ingiza mai Kantu suke ma wasu Talakawa.
Babban Abin da ke Ban Sha’awa da Gwamnatin Ganduje, shine yadda duk aikin da zai yi domin al’umma ya ke ba Dan Kan sa ba Sabanin Gwamnatin da ta shude, inji shi.