Kano na cin gajiyar masu yi wa kasa hidima da aka saka a jihar inji Ganduje
Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce Kano na cin gajiyar masu yi wa kasa hidima da aka tura jihar tun lokacin da aka fara shirin NYSC.
Dr. Ganduje Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin bikin karrama masu bautar Kasar rukunin A na shekarar 2021, Wanda ya gudana a filin a wasanni na Jami’ar Bayero Kano.
Gwamnan wanda mataimakinsa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya wakilta ya kuma jinjina wa ’yan kungiyar da cewa…
“wannan tsarin ya yi nasarar ginawa magabatansu kyakkyawar Makoma, ta hanyar bayar da gudunmawa a ayyuka daban-daban na ci gaban al’umma, musamman a fannin kiwon lafiya, ilimi da muhalli, da kuma tsafta, don haka al’ummar Jihar Kano za su rika tunawa da ku.”
Dr. Gawuna Ya ci gaba da cewa zaman da suka yi a Kano a shekara daya da ta gabata ya kafa hadin kai tare da tunkarar kalubalen rayuwa da sabbin kwarewa a fagage daban-daban na nema.
Sai dai Gwamnan ya gargade su da su yi amfani da dabarun da suka koya don samar wa kansu dukiya ta yadda za su zama masu daukar ma’aikata maimakon masu neman aiki.
A nata jawabin shugabar hukumar NYSC ta jihar Hajiya A’isha Tata Muhammed ta bayyana cewa daga cikin masu yi wa kasa hidima 889 da aka shirya yayesu, 3 sun bambanta da sauran a fannin ayyukan ci gaban al’umma wanda ya ba su lambar yabo ta jiha yayin da ‘yan kungiyar 16 za su samu lambar yabo.