Hukumar dake kula da shige da fice watau Custum, tace Jirage 30 cikin sittin da aka tantance za su baiwa gwamnatin tarayya haraji. Kamar yadda Jaridar Daily Nigerian ta wallafa a shafinta
Mai magana da yawun hukumar ta NCS, Joseph Attah, ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja.
Mista Attah, yace dayawa daga cikin wadannan jiragen suna shigo da kayayyaki ne cikin kasar nan na wucen gadi, wanda wannan ya basu damar shigowa da jiragen.
KARANTA:- Sakamakon ba EFCC rahoton karya: An iza keyar mutane 2 zuwa gidan kaso
Ya cigaba da cewa da akwai da yawan su wadanda suka daina biya haraji baya alkwarin ya Kare, wanda haka ya janyo sai da aka tantance su.
Mai magana da yawun hukumar yace yin tantancewar ya sanya hukumar ta gano jiragen da suke cikin kasar nan na Yan kasuwa da kuma wadanda na hawa ne kawai.
Mista Attah yace, anyi wannan tantancewar ne badan aci mutuncin wani ba, sai dan a samar ma da gwamnatin tarayya kudaden shiga.
Da kuma tabbatar da cewar an anso kowane haraji an damkashi ga gwamnatin tarayya.
“Kamar yadda kuka sani ne, kasar nan na cigaba da fuskantar matsaloli na talkain arziqi, karbar haraji zai taimaka sosai musamman wajan tsaro.” Kamar yadda yace
Yin hakan shi zai bada damar sanin jiragen dake shigo da ficewa
Ya cigaba da cewa, duk da sati biyun da aka Kara na biyan harajin, an kara sanya wasu sati biyun tun daga 26 na watan July har zuwa 6 ga watan Agusta.
Kwantrola na kwastom ya kara sati biyunne duba da jiragen da ake tantancewa da kuma wadanda suka cancanta da su biya haraji cikin wannan kasar.
Mun riga mun sani cewar manyan mutane ne a Najeriya keda mallakin jiragen sama, shiyasanya ma dole mu dauki mataki yadda ya kamata, shiyasa mukayi tunanin kara lokacin biyan harajin.
Yace wannan zai zama lokacin na karshe, ba za a kara daga wani lokaci ba, duk mai Jirgin da bai biya haraji ba to tabbas za’a rike Jirgin.