Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya roƙi sabon shugaban Amurka Joe Biden ya taimakawa Nijeriya wajen yaki da ta’addanci da matsalar tsaro da ya addabi kasar.
Atiku ya nemi hakan ne a wani sakon sakon Twitter da ya wallafa, inda ya ce ya yi imanin cewa wannan sabon shugabancin da aka shiga a Amurka zai sake dawo da martaba da mutuncinta a matsayin tushen dimokradiya a duniya.
Sannan ya na fatan ganin ƙyaƙyawan dangantarka da ke tsakanin kasashen biyu ta dore domin cin gajiyar kowanne ɓangare.
A karshe ya kuma mika sakon taya murna ga sabon shugaban Amurka na 46 Joe Biden.