Malamin addinin musulunci mazaunin Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi kira ga hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta saki Tukur Mamu, ko kuma ta gurfanar da shi a gaban kotu.
Da yake bayar da misali da dokar, Gumi ya ce duk wanda aka kama bisa aikata laifin akwai bukatar a gurfanar da shi gaban kotu cikin sa’o’i 24.
KARANTA WANNAN LABARIN: IPOB Ba Za Ta Iya Yiwa Buhari Wata Barazana Ba — Gwamnatin Imo
Jaridar DIMOKURADIYYA ta rawaito yadda aka kama Mamu, wanda shine mai shiga tsakanin wajen ganin a sako wasu daga cikin wadanda harin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja ya rutsa da su a filin jirgin sama na Alkahira a hanyarsa ta zuwa kasar Saudiyya don gudanar da aikin Hajji.
An dawo da shi, wanda kuma DSS ta kame shi shi a filin jirgin sama na jihar Kano.
Daga baya hukumar DSS ta ce Mamu na da tambayoyi da zai amsa kan matsalar rashin tsaro a kasar.
A yayin wa’azin mako-mako a masallacin Sultan Bello, Gumi ya ce an kama Mamu ne saboda rawar da ya taka wajen taimaka wa wadanda harin ta’addanci ya shafa.
Malamin wanda ya ce Allah yana da hanyar gwada mumini, ya kara da cewa kamun da aka yi wa Mamu hanyar Allah ce ta gwada imaninsa, inda ya yi addu’ar Allah ya kubutar da Mamu.
“Ku kai shi kotu a bar Kotu ta fuskanci shari’a, tsare shi a gidan yari duk da kasancewarsa dan uwa ne kawai don tsoratar da shi. Wannan tsoratarwa kuma ta’addanci ce. Kame mutane bisa zalunci, shi ma ta’addanci ne; kamar yadda ‘yan ta’addan ke yi ta hanyar zuwa gidan wani su yi garkuwa da shi.”
“Ta yaya za mu ci gaba a cikin wannan yanayi a karkashin gwamnatin da ke shirin kawo karshe? Fatanmu shine a gama su cikin nasara ba cikin mummunan yanayi ba.”
“Ba batun Tukur Mamu ba kun san cewa duk lokacin da suka kama mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, na kan yi magana ne, ba wai maganar wani da na sani ba kuma Ina ba gwamnati shawara ce kawai ta sake shi domin mu ba shi hakuri ya manta da abin da ya faru.”
A wani labarin kuma, Wike Ya Karbi Daruruwan Masu Ficewa Daga APC A Jihar Rivers
Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas a ranar Asabar din nan ya tarbi daruruwan masu sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulkin kasa zuwa jam’iyyar PDP mai mulki a jihar.
Wadanda suka halarci taron a Fatakwal, babban birnin jihar sun hada da shugaban jam’iyyar PDP na jihar Rivers, Desmond Akawor; tsohon dan kwamitin amintattu na jam’iyyar APC, Sam-Sam Jaja; tsohon kwamishinan wasanni, Fred Igwe; da daruruwan magoya bayansu.