Akwai rashin tabbas kan barazanar da kamfanonin jiragen suka yi na dakatar da aiki sakamakon tashin gwauron zabin da man jiragen da aka fi sani da Jet A1.
‘Yan kasuwar man da dillalan kamfanin sun kasa cimma matsaya kan sabon tsarin farashin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Taron da kamfanonin jiragen sama na Najeriya (AON) da masu sayar da man jiragen sama suka yi don samar da sabon tsarin farashin man jiragen wanda ya kawo cikas ga ayyukan jiragen a cikin ‘yan makonnin da suka gabata ya kare ba tare da isa ga tsarin farashi mai kyau ba.
Taron ya samu halartar kamfanonin jiragen sama da masu samar da man fetur da dama tare da babban Daraktan, kamfanin kula da kuma tasarrufin man fetur din, Mista Ogbugo Ukoha.
Haka kuma a wajen taron akwai Babban Daraktan Rukunin na Kasa na Kamfanin Mai na Najeriya (NNPC), Mista Adeyemi Adetunji.
Hakan dai ya biyo bayan taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a majalisar wakilai inda aka amince cewa za a sayar da man jirage a kan Naira 500 ga kowace lita na tsawon kwanaki uku yayin da masu aiki za a ba su lasisin shigo da mai.
Domin fito da samfurin farashi mai karbuwa, AON da dillalan man fetur da kungiyar (MOMAN) da kungiyar dillalan man fetur ta kasa (MOMAN) da (DAPPMAN) suka wakilta da wakilan kamfanin NNPC suka gana inda bangarorin biyu suka bayyana matsayinsu.
Shugaban Kamfanin Jiragen Sama na United Nigeria Airlines, Cif Obiora Okonkwo, wanda ya yi magana a madadin kamfanonin jiragen, ya dage kan cewa sayen man fetur sama da Naira 500 kan kowace lita ba abu ne mai dorewa ba, yana mai cewa babu wani dan Najeriya da zai iya tashi idan kamfanonin jiragen sun kara kudin tikitin jirgi.
Okonkwo ya ce zirga-zirgar jiragen sama na zaman jama’a ne, kuma rufewar zai shafi kowane fanni na tattalin arziki, yana mai jaddada bukatar duk wani nau’i na shiga tsakani daga gwamnatin tarayya domin kaucewa rikicin da ke kunno kai.
Binciken da Daily Trust ta gudanar ya nuna cewa ana sayar da man jiragen sama tsakanin Naira 570 zuwa 607 kan kowace lita a fadin kasar nan.
Rushewar farashin farashi a yankuna ya nuna cewa N570 ne a Legas; N579 a Abuja da Fatakwal da kuma N607 a Kano.