By Ishaq Dabai
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya bayyana Mista John Ugbe na MultiChoice Najeriya, na Babban Kamfanin Nishaɗi na Afirka, a matsayin wanda ya lashe kujerar Shugabancin Ƙungiyoyin yada Labarai ta Najeriya (BON) wanda hakan babbar nasara ce ga masana’antar yada labarai.
A cikin Wata sanarwa da Malam Mohammed Garba, kwamishinan yada labarai na gwamnan kano ya fitar, ta yaba da zaben da aka gudanar a dakin taro na gidan gwamnatin Kano, a wurin da za a gudanar da taron kungiyar karo na 75 bisa zaman lumana.
Ya umarci sabon shugaban da ya yi aiki tare da masu ruwa da tsaki da suka dace don matsar da yada shirye shiryen zuwa mafi girman matsayi musamman a yayin da ake fuskantar kalubale na duniya.
Ganduje ya lura cewa haduwar kungiyoyin yada shirye shirye na gwamnati da masu zaman kansu abin alfahari ne ga masana’antar a daidai lokacin da Najeriya ke fuskantar canjin fasaha.