Mai martaba Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya ya kaiwa Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, ziyarar godiya, inda kuma aka tarbe shi da tawagarsa a babban dakin taro na Coronation dake gidan Gwamnati.
Mai Martaba Sarkin Gaya ya kai ziyarar ne tare da daukacin masu rike da sarautar Gargajiya na masarautar Gaya tare da Shugabbannin kananan hukumomin yankin.
A jawabin sa, Sarkin Gaya ya godewa Gwamnan bisa cika masa burin sa da yayi na gadon mahaifin sa, inda ya bayyana hakan a matsayin abinda bazai taba mantawa da shi ba.

Da yake bayyana irin nasarorin daya samu daga lokacin da aka nada shi zuwa yanzu, sarkin Gaya yace sun sami nasarori da dama, musamman akan harkar tsaro da ilimi inda yake iya zuwa da kan sa domin ganin yadda makarantun yankin suke.
KARANTA WANNAN LABARIN: CBN da SEC Sun Ƙaƙabawa wasu bankuna 20 takunkumi
Gwamnan ya godewa sarkin na Gaya da daukacin yan fadar tasa inda ya bayyana nasarorin da Sarkin ya samu a matsayin abin alfahari da kuma bashi goyon baya don cimma kyawawan kudirin sa na ganin an ciyar da masauratar gaba, inda yace wadannan abubuwan na daga cikin dalilan da suka saka shi kirkirar sabbin masarautun.

Yayin ziyarar, Gwamnan yana tare da mataimakin sa, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna; kwamishinan kananan hukumomi da harkokin masarautu, Hon. Murtala Sule Garo; Sakataren Gwamnati, Alhaji Usman Alhaji da sauran jami’an Gwamnati.
