By Ishaq Dabai
Akalla matasa 4,400 zuwa yanzu suka tsunduma cikin jihar Kano don fara gangamin wayar da kan jama’a na gida-gida don tabbatar da canjin ɗabi’a akan wanke hannu da ingantattun hanyoyin tsafta don yaƙar yaduwar cutar COVID-19 a jihar.
Manajan Darakta na Hukumar Samar da Ruwa da Tsaftar Ruwa, Ibrahim Bichi ne ya bayyana haka a Kano ranar Talata a zaman wani bangare na bikin ranar wanke hannu ta duniya a jihar.
Bichi, wanda Daraktan tsare -tsare da hada kan al’umma, Yusuf Abdullahi ya wakilta, yace matasan da adadinsu ya kai 100 daga cikin kananan hukumomi 44 zasu zama masu kawo canji ta hanyar wayar da kan mutane kan yadda zasu tsaftace muhallin su.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa, “Zuwa yanzu, matasan sun kai gidaje guda 130,000,kuma aiki yana cigaba da gudana a fadin jihar.
“shugaban ya yi bayanin cewa an tsara shirin ne domin sanya matasa 100 su shiga cikin kananan hukumomi 774 da ake dasu a fadin tarayya.”