Masu garkuwa da mutane sun sako Dodo na Wawa, Dr Mahmoud Ahmed Aliyu bayan ya kwashe kwanaki 45 a hannun su.
Rahotanni sun nuna cewa, cewa, an sake shi da misalin karfe 7:30 na yammacin jiya Talata, bayan biyan kudin fansa Naira Milliyan 10.
Wazirin garin Wawa, Alhaji Ja’afar Ibrahim Bio, ya tabbatar wa da Jaridar Daily Trust sakin Basaraken Gargajiyan ta wayar tarho, amma ya ki yin karin bayani kan nawa aka biya don sakin sa.
A wani faifan bidiyo da iyalansa suka raba wa majiyar Jaridar Dimokuradiyya, an ga basaraken a cikin farin rawani, yayin da iyalansa da mambobin fadar ke maraba da shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dan Takarar Gwamnan a Yobe ya yi Murabus daga Jam’iyar APC
Wani dan uwansa da ya fara bayyanawa wa wakilinmu labarin sakinsa, ya yi addu’a ga Majiyar mu dangane da don rahoton da tayi na halin da mahaifinsu ya shiga.
Idan za’a iya tunawa dai, Wasu manyan mutane dauke da muggan makamai sun sace Aliyu a fadarsa da misalin karfe 9 na dare, a ranar 4 ga watan Satumban shekarar nan.
A wani labarin na daban.
Akalla matasa 4,400 zuwa yanzu suka tsunduma cikin jihar Kano don fara gangamin wayar da kan jama’a na gida-gida don tabbatar da canjin ɗabi’a akan wanke hannu da ingantattun hanyoyin tsafta don yaƙar yaduwar cutar COVID-19 a jihar.
Manajan Darakta na Hukumar Samar da Ruwa da Tsaftar Ruwa, Ibrahim Bichi ne ya bayyana haka a Kano ranar Talata a zaman wani bangare na bikin ranar wanke hannu ta duniya a jihar.
Bichi, wanda Daraktan tsare -tsare da hada kan al’umma, Yusuf Abdullahi ya wakilta, yace matasan da adadinsu ya kai 100 daga cikin kananan hukumomi 44 zasu zama masu kawo canji ta hanyar wayar da kan mutane kan yadda zasu tsaftace muhallin su.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa, “Zuwa yanzu, matasan sun kai gidaje guda 130,000,kuma aiki yana cigaba da gudana a fadin jihar.
“shugaban ya yi bayanin cewa an tsara shirin ne domin sanya matasa 100 su shiga cikin kananan hukumomi 774 da ake dasu a fadin tarayya.”