Shugaban Kungiyar Dillalan man fetur Na Kasa Reshen Jihar Kano Alhaji Bashir Dan Malam Ya Bayyana Cewa Daga Yanzu Zuwa kowane Lokaci manfetur Zai wadata a Birnin kano Da Kewaye.
Barshir Dan Malam yayin ganawarsa da manema labarai, Yace amfara shawo Kan Matsalar Da Ta kawo Rashin man Fetur Din Da Ya shafi Rayuwar Al’ummar Jihar Kano Da Ma Kasa Baki Daya.
Ya Cigaba Da Cewa Ya kamata Al’umma Su Rika yi musu Adalci maimakon Zagi Da Kuma Kausasan Kalamai, Yana Mai Cewa Basa Boye Mai Kamar Yadda Mutane Ke zarginsu.
Ya Cigaba Da Cewa Mutane suna amfani Da Man Fetur Sosai Dan Haka ko yaya aka samu tsaiko sai an samu Karancinsa.
Ya Bayar da Tabbacin Cewa Zuwa Yanzu Manyan Motoci Dauke Da Manfetur sun Fara Shigowa Kano kuma Hatta Babban Ofishin NNPC Dake Hotoro ya Fara Rabawa masu Gidajen mai Fetur din Domin samun saukin wahalar sa Ga Al’umma.