Majalisar dokokin karamar hukumar Bida ta jihar Neja ta dakatar da shugaban karamar hukumar Bida Dr Suleiman Sheshi.
Jaridar Dimokuradiyya ta samu wasikar dakatarwar mai dauke da kwanan wata 8 ga watan Nuwamba, 2021, kuma aka aika wa gwamnan jihar, Abubakar Sani Bello.
Shugaban majalisar Nma Alhaji Shehu ne ya sanya wa takardar hannu.
Kansilolin sun ce an dakatar da shugaban karamar hukumar na tsawon watanni shida bisa wasu laifuka uku da suka hada da karkatar da kudaden kananan hukumomi da aiwatar da ayyuka ba tare da neman amincewar majalisar ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jami’ar Lokaja Ta Dauki Mafarauta 60,
“Shugaban zartaswa yana karkatar da kudaden kananan hukumomi ba tare da amincewa majalisar dokoki ba,”inji wani bangare na wasikar.
Majalisar ta amince da matakin dakatarwar tare da sanya hannun kansiloli 12 cikin 14 na majalisar.
An aika kwafin wasikar zuwa majalisar dokokin jihar, ma’aikatar kananan hukumomi, hukumomin tsaro da dai sauransu.